Accessibility links

Sakatariya Hillary Clinton zata gana da shugabannin Isra'i'la da Falasdinu


Sakatariya Amurka Hillary Clinton

Yau litinin ake sa ran sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton zata gana da jami’an Isra’ila da na yankin Falasdinu.

Yau litinin ake sa ran sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton zata gana da jami’an Isra’ila da na yankin Falasdinu. Shawarwarin da zasu yi maida hankali ne kan shirin zaman lafiya tsakanin su, ci gaba da aka samu a Masar, al’amura a Syria da kuma Iran.

Sakatariya Clinton ta gana da shugaban yankin Falasdinu Mahmoud Abbas a fara rangadin kusan makonni biyu da zata yi a yankin.Tana son ta tattauna da shugabannin Isra’ila kan wasikun da sassan biyu suka yi musaya a baya bayan nan, yayinda ake ci gaba da shirin wanzar da zaman lafiya ba tare da sassan biyu sun zauna teburi daya ba.

Sakatariya Clinton tayi tattaki zuwa birnin kudus daga Masar, inda ta tattauna batun tallafin ta fuskar tattalin arziki da shugaba Morsi da Field Marshall Mohammed Hussein Tantawi. Wakilin Muryar Amurka Scott Stearns wanda yake cikin ‘yan jarida dake tafiya da sakatariya Clinton, yace dukkan shawarwari da zata yi a Isra’ila zasu tabo batun rawar da Masar zata taka wajen ganin an tabbatar da zaman lafiya a yankin, da kuma tabbacin da Mr. Morsi ya baiwa sakatariya Clinton cewa Masar zata mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da Masar ta kulla da Isra’ila a 1979.

XS
SM
MD
LG