Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Musulmi Ya Kira A Mayar da Hankali Wajen Inganta Tattalin Arziki


Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar

Sarkin Muslmi Sultan Sa'ad Abubakar ya yi kira a Minna da a mayar da hankali akan habaka tattalin arziki domin inganta rayuwar al'umma da zata sa mutane ba zasu damu da wake shugabancin kasar ba.

Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Sultan Sa'ad Muhammad Abubakar ya yi kira da a maida hankali wajen bunkasa tattalin arziki da zai sa 'yan kasar su kasance cikin walwala.

Yayinda yake jawabi a wani taron bunkasa kasuwanci a Minna babban birnin jihar Neja yana mai cewa kamata yayi 'yan Najeriya su maida hankali wajen kiran a yi kokarin bunkasa tattalin arziki.

Inji Sarkin, "na yi imani idan muka maida hankali wajen yin magana akan a bunkasa tattalin arziki zai taimaka domin kuwa idan tattalin arziki na tafiya yadda ya kamata babu wanda zai damu da wa yake mulkin wani"

Mai sharhi kan alamuran kasa kuma shugaban cibiyar bincike da nazarin al'adun kimiya da fasaha dake Minna Ahmed Ibrahim Khalil yace maganar Sarkin Musulmi tana kan hanya "to amma akwai wani hanzari ba gudu ba"

Yana mai cewa matsalar Najeriya ba ta tattalin arziki ba ne ta rashin shugabanci ne saboda babu iyaye. A da can baya ana anfani da shugabannin gargajiya da na addinai amma yanzu an ciresu daga harkokin kasar, inji Khalil. A cewarsa kowa ya yi kudi yanzu shi ma sarki ne.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG