Accessibility links

Satar Mutane a Najeriya


Hoton wani gida kennan, inda aka rike wasu mutane da aka sata a jihar Sokoto.

Rahotannin dake fitowa daga Nijeriya na cewa wasu ‘yan bindiga da ba’a tantance suba, sun sace uwargidan daya daga cikin manyan Alkalan babbar kotun Nigeria tare da ‘yarta da kuma direbansu.

WASHINGTON, D.C - Kafofin labarun Najeriya sun ji daga bakin manyan jami'an Gwamnatin Nigeria na cewa a daren Juma'ar da ta gabata ce aka gudanar da wannan ta'asar a jihar Edo dake kudancin Nigeria.

Jami'an Najeriya sun kara da cewa uwargidan babban Alkalin da ‘yarta da kuma direben mota suna kan hanyarsu ta zuwa Benin, babban birnin jihar Edo domin halartar bikin auren ‘yar babban alkalin da ake shirin yi lokacin da ‘yan bindigar suka yi masu kwanton bauna, suka bullowa motar da suke ciki ba zato ba tsammani a tsakiyar hanya. Tilas direban motar ya ja ya tsaya.

Ya zuwa yanzu dai ‘yan bindigan basu tuntibi Alkalin babbar kotun Najeriya mai shari’a Bode Rhodes-Vvours ba, balle a san irin halin da iyalan Alkalin suke ciki. Babu kuma wata bukata ta musamman da ‘yan bindigar suka gabatar.
XS
SM
MD
LG