Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudiyya za su tsagaita wuta a Yamal


Wasu tarwatsastsun rukunin kasuwancin da aka tarwatsa a Yamal

Sojin taron dangin da Saudiyya ke jagoranta wajen yakar ‘yan Houthis a Yamal, sun ce zasu tsagaita wutar jin tausayin bil’adama na kwanaki 5 a kasar Yamal.

Wannan tsagaita wutar zai fara aiki ne da tsakar daren yau Lahadi. Tsagaita wutar ta biyo bayan bukatar shugaban kasar mai gudun hijira a kasar Saudiyya Abd-Rabbu Mansur Hadi.

Ya roki haka don a sami kai kayan agaji a Yamal, kamar yadda sanarwa ta fito a kafar talbijin ta Saudi Arabia. Sai dai sojojin taron dangin suna da damar maida martini matukar ‘yan Houthis ko makamantansu suka kai farmaki a lokacin tsagaita wutar.

Labarin tsagaita wutar kuma ya biyo bayan luguden wuta da aka yiwa birnin Taiz ta sama a ranar Asabar ya hallaka fararen hula kimanin 35 da jikkata da dama. Majalisar Dinkin Duniya tace rikicin watanni 4 Yamal din ya hallaka akalla mutane 3,640 rabinsu fararen hula.

XS
SM
MD
LG