Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sengal Ta Shiga Jerin Kasashe Dake Neman Gadhafi Yayi Murabus

Wani dan tawaye yake magana da na'urar sadarwa a wani fagen daga a birnin Misrata.

A halin yanzu kuma…shugaban kasar Senegal yayi kira akan shyugaban Libya din Muammar Ghadafi da ya yi murabus, har yana cewa “saukarka da sauri itace mafi alheri ga kowa.”

A halin yanzu kuma…shugaban kasar Senegal yayi kira akan shyugaban Libya din Muammar Ghadafi da ya yi murabus, har yana cewa “saukarka da sauri itace mafi alheri ga kowa.”

A yau ne shugaba Abdoulaye Wade yake wannan kiran a birnin Benghazi ta Libya inda shima yaje yana ganawa da jagabannin ‘yantawayen Libyar. Shugaba Wade yace shi yana iya taimakawa Ghadafi ya sauka daga mulki, koda yake bai fito balo-balo yayi mishi tayin bashi mafaka a can kasarshi ta Senegal ba.

Senegal dai tana daya daga cikin kasashe da daman a duniya da suka rungumi kuma suka amince da majalisar mulki da kungiyar ‘yantawayen Libyar ta kafa.

XS
SM
MD
LG