Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Ganawar Shugaba Buhari da 'Yan Majalisun APC Tayi Tasiri


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

A wannan makon ne shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya gana da 'yan majalisun jam'iyyarsa da nufin kawo karshen barakar da ta kunno kai tsakaninsu.

Abokin aiki ya tuntubi Malam Sufiyanu A-Sadiq Saidu mai nazari akan harkokin siyasa, musamman irin ta Najeriya.

Alamar tambaya nan ita ce shin ganawar da shugaba Buhari ya yi dasu tayi tasiri, wato an samu shawo kan 'yan majalisun an dinke barakar. Malam Safiyanu ya fara da cewa akwai rahotanni dake cewa wasu daga cikin iyayen jam'iyyar suna da karfi da yawa kuma kamata yayi a karyasu. Daya daga cikinsu shi ne Ashiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda suk gani ya zama alakakai.Irin wadannan masu ra'ayin babu yadda zasu yadda a canza shugabancin majalisun biyu.

Masu ra'ayin a ragewa irin su Tinubu karfi su ne suka sabawa matsayin jam'iyyar a zaben shugabannin majalisun. Su ne suke goyon bayan shugaban majalisar dattawa Olusola Saraki da shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara. A wurinsu kasancewar wadannan shugabannin akan kujerunsu shi ne daidai.

Akan zaman da suka yi jiya da shugaban kasa saboda dinke barakar dake tsakaninsu yace wadanda suka ce lallai a yiwa jam'iyya biyayya suma sun ja tunga. Suna nan kan bakarsu. Amma a bangaren majalisar wakilai kamar sun yi amai sun lashe domin Gbajabiamila ya zamo shugaban masu rinjaye kamar yadda jam'iyyar ta bukata. Amma a majalisar dattawa lamarin bai canza ba.

Safiyanu yace na ciki na ciki na baka kuma na baka. Jam'iyyar zata yi kokari ta nuna komi ya kankama amma bayan wani dan lokaci barakar zata fito fili.Misali idan APC ta amince da shugabancin Olusola Saraki babu yadda zata amince da shugabancin mataimakinsa wanda dan jam'iyyar PDP ne. Yanzu dai tana kasa tana dabo

XS
SM
MD
LG