Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Gaskiya Ne Akwai Baraka Tsakanin Bola Tinubu da Shugaba Buhari?


Ahmed Bola Tinubu
Ahmed Bola Tinubu

Watanni da dama ba’a ga Bola Tinubu yana cikakkiyar muamala da shugaban kasa Muhammad Buhari ba, abun da ya sa masu hasashe kan al’amuran siyasa da na yau da kullum ke ganin kamar akwai baraka tsakaninsu ne

Bayan watanni da dama da ba’a ga madugun siyasar Yarabawa Bola Tinubu a Fadar Shugaban kasa ba, sai ga shi jiya ya bayyana har ya yi ganawa ta siri da Shugaba Muhammad Buhari.

Bayan ganawar tasu, manema labarai sun tambayi Bola Tinubu ko akwai baraka tsakaninsa da Shugaba Muhammad Buhari? Tinubu yace labarin kanzon kurege ne tare da cewa shi yana da gwarin gwuiwa akan gwamnatin Buhari.

Amma ya amince da cewa akwai wasu abubuwa da idan sun faru sukan jayo rade radi, amma bai fayyace abubuwan ba.

Sai dai Shu’aibu Mungadi, mai sharhi kan harkokin Najeriya yace ba lallai ba ne Bola Tinubu ya goyi bayan shugaban kasa a zabe mai zuwa ba, ganin cewa yadda ya so a gudanar da mulkin kasar dashi hakan bai samu ba. Mungadi yace rashin samun wannan damar ka iya sa ya nisanci mulkin shugaba Buhari.

Shi ma Muhammad Ibrahim, wanda ya kware akan harkokin ‘yan siyasa, ya maimaita kalaman da shugaban kwastan da uwargidan Shugaba Buhari suka taba fada, na cewa wadanda ba’a yi gwagwarmayar neman zabe da su ba, sune yanzu suka kewaye shugaban kasan, suna kuma juya akalar tunanensa.

A nasa ra’ayin, wani mai sharhi, Dr. Kabiru Danladi Lawanti, yace mai yiyuwa ne Bola Tinubu taka-tsantsan ya keyi a siyasance saboda yana gudun kada a ce su ne suke juya shugaban kasa.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:29 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG