Accessibility links

Shugaba Obama ba Zai Gana da PM Isra'ila Benjamin Netanyahu ba

  • Aliyu Imam

Shugaba Obama da Firayim Minista Isra'ila Benjamin Netanyahu.

Fadar Shugaban Amurka ta White House ta bayyana cewa Shugaba Barack Obama ba zai gana da Firayim Minista Benjamin Netanyahu, a lokacin da shugaban Isra’ilan zai kawo ziyara nan Washington a farkon watan Maris domin yin jawabi da kuma ganawa da gamayyar majalisun dokokin Amurka.

Wata mai magana da yawun Kwamitin Tsaron Kasar, ta bayyana jiya Alhamis cewa tun shekaru masu yawa da suka wuce, shugaban Amurka baya ganawa da shugaban wata kasa da ake daf da zabe a kasarsa. Mr. Netanyahu zai zo nan Amurka ran 3 ga watan Maris, makonni biyu kafin zaben da zai kara neman wa'adi domin cigaba da zama Firayim Minista Israila.

Martanin Fadar White House ta biyo bayan sanarwar da abokin hamayyar Mr. Obama, Speaker John Boehner, yayi mai cewa, ya gayyato shugaban Yahudawan ne domin ya bayyanawa majalisun irin barazanar masu tsatsaurar ra’ayin addinin Islama, da kuma Iran suke yiwa Amurka.

Boehner, dai ya gayyaci shugaban Isra’ilan ne ba tare da tuntubar fadar White House ba, lamarin da yasa wani mai magana da yawun shugaba Obama yace ya keta sharrudan da ake bi wajen gayyatar shugaban wata kasa.

Wasu ‘yan majalisar dokoki daga jam’iyyar Republican, da wasu daga jam’iyyar Democrat na yunkurin gani an kara zafafa takunkumai akan Iran ne, domin matsanta mata lamba ta kawo karshen hada makaman Nukiliyarta.

Mr. Netanyahu ya sha furta damuwarshi cewa kasar Amurka da sauran kasashe biyar da suka fi karfi a duk fadin duniya na yiwa shawarwarin da akeyi da Iran rikon sakainar kashi.

Mr. Obama bai amince da karawa Iran takunkumai ba, kuma ya gayawa ‘yan majalisa a taronsa na shekara shekara Talatan data shige cewa idan majalisun suka amince akan sababbin takunkumai, to zai hau kujerar naki.

XS
SM
MD
LG