Jiya asabar hukumar zabe ta Zimbabwe ta ce Mr. Mugabe shi ya lashe wannan zabe inda ya samu kashi 61 cikin 100, yayin da dadadden abokin hamayyarsa firayim minista Morgan Tsvangirai ya samu kashi 34 cikin 100 kacal. Mugabe zai kara yin wasu shekaru 5 a kan karagar mulki.
Haka kuma, jam’iyyar ZANU-PF ta Mr. Mugabe ta lashe fiye da kashi biyu bisa uku na kujerun majalisar dokoki, abinda zai ba ta sukunin sauya tsarin mulkin kasar idan tana bukatar hakan. Jam’iyyar MDC ta Mr. Tsvangirai ta samu kujerun da ba su taka kara sun karya ba a cikin wannan majalisa mai wakilai 210.
Mr. Tsvangirai dai yayi tur da zabubbukan na shugaban kasa da ‘yan majalisar dokoki, yana mai bayyana su a zaman na bogi, yana mai lasar takobin shekawa zuwa kotu domin kalubalantar sakamakon tare da kiran a sake zabe.
Mr. Tsvangirai ya shaidawa taron ‘yan jarida cewa jam’iyyarsa ba zata shiga cikin sabuwar gwamnati ba.
Kiyawar da jam’iyyar MDC ta yi ta amince da sakamakon zaben ta haddasa fargabar cewa ana iya sake ganin irin mummunan tashin hankali da zub da jinin da suka biyo bayan zaben da aka yi gardamarsa a shekarar 2008.
Su ma wasu kasashen waje sun bayyana damuwa game da zaben.