Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Ja Kunnen Israila Akan Fadada Gine-gine A Yankin Falasdinawa


Sean Spicer kakakin shugaban Amurka
Sean Spicer kakakin shugaban Amurka

Fadar White House ta shugaban Amurka ta Fada jiya Alhamis cewa, kara fadada gine gine a yankunan ‘yan share-wuri-zauna ya wuce bakin iyakarta na yanzu da kasar Israila take yi, ba zai taimaka ba wajen samar da zaman lafiya tsakanin Israilan da Palesdinu.

Sai kuma mai Magana da yawun Fadar ta White House Sean Spicer yace duk da yake gwamnatin Trump bata amince cewa gine-gine a yankunan da Isra’ila ta mamaye yana hana cimma zaman lafiya ba, sai dai kuma kawo yanzu gwamnatin ta Trump bata dauki matsayi a hukumance ba game da wannan batu na ‘yan share wuri zauna ba.

Duk da haka Spicer yace Shugaba Trump yana hankorontattaunawarda zai yi da Firayim Ministan na Israila Benjamin Netenyahu sailin da zai kawo ziyara a nan Washington DC wani lokaci cikin wannan watan da muke ciki.

Palesdinawa suka ce sansanonin ‘yan share wuri zauna a yammacin kogin Jordan da suke so ya zaman bangaren kasarsu da za’a kirkiro nan gaba, shine ke kawo tsaiko wajen samar da zaman lafiya.

Yayinda ita kuma Israila tace kin da Palesdinu tayi ne na diyaucin bani- Yahudun shine babban abinda ke kawo wa tattaunawar cikas.

Kasar Israila tayi fusata kwarai da gaske lokacin da tsohuwar gwamnatin Amurka a karkashin shugaba Barrack Obama ta kauracewajefa kuri’a kan wani kudurin kwamitin sulhu naMDD maimakon ta hau kujerar naki, kudurin da yace gine-gine a yankunan Falasidnu da Isra’ila ta mamaye basa bisa ka’ida, kuma ta bukaci Isra’ila ta tsaida ayyukan baki daya.

XS
SM
MD
LG