Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Angola Yace Ba Zai Sake Neman Wa’adin Mulki Ba


Shugaban kasar Angola Jose Eduardo dos santos ya fada yau jumma’a cewa, ba zai sake neman wani wa’adin shugabanci ba a bana, abin da zai kawo karshen mulkinsa na kusan shekaru talatin da takwas.

Dos Santos ya shaidawa wani taron jam’iya mai mulki MPLA cewa, ministan tsaron kasar Joas Lourenco shine zai kasance dan takarar jam’iyar na farko a zaben da za a gudanar a watan Agusta.

Dos Santon dan shekaru saba’in da hudu, ya bayyana a lokutan baya cewa, zai sauka daga karagar mulki. Ya fara shugabancin kasar Angola a watan Satumba shekara ta dubu da dari tara da saba’in da tara, ya kasance shugaban kasar Afrika na biyu a jerin wadanda suka fi dadewa bisa karagar mulki, bayan Teodoro Obiang na Equatorial Guinea.

A karkashin shugabancin Dos Santos, Angola ta sami makudan kudaden shiga daga albarkatun mai, ta kuma kawo karshen yakin basasa, sai dai kungiyoyin kare hakin bil’adama suna zarginsa da keta hakin bil’adama da kuma kazamin azurta kansa.

Watan da ya gabata, mujallar Fobes ta ambaci ‘yar shugaban kasar Isabel dos Santos a matsayin wadda tafi kowacce mace arziki a nahiyar Afrika, inda ta mallaki dala miliyan dubu dari uku da ashirin.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG