Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Brazil Ya Ki Sauka a Mulki


Shugaban Brazil Michel Temer
Shugaban Brazil Michel Temer

Ana ci gaba da kai ruwa rana a Brazil, yayin da shugaban kasar Michel Temer ya yi kememe ya ce ba zai sauka akan karagar mulki ba, duk da cewa ana zarginsa da laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa.

Shugaban kasar Brazil Michel Temer ya ki sauka daga karagar mulki duk da yiwuwar fuskantar tuhuma, bisa zargin cin hanci da rashawa da kuma dushewar tauraronsa a idanun al’ummar kasar.

Wani binciken ra’ayoyin jama’a da aka gudanar ya nuna cewa, goyon bayan da yake da shi ya yi kasa ainun zuwa kashi bakwai cikin 100.

Daga cikin ababan da suka fara karya lagwan shugaban, akwai batun zaftare kudin fensho da kuma gudanar da wasu sauye-sauye yayin da yake kokarin fitar da kasar daga matsalar komadar tattalin arziki da take fuskanta.

A yau Talata ake sa ran, babban mai shigar da karar kasar Brazil zai bayyana matsaya, kan ko za a tuhumi Temer da laifin zarmiya, da karbar toshiya, da hana doka aikinta da kuma zama mamban wata kungiya mai aikata miyagun laifuka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG