Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Rasha Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa A Karo Na Hudu


Shugaban Rasha Vladimir Putin bayan da ya kada tashi kuri'ar
Shugaban Rasha Vladimir Putin bayan da ya kada tashi kuri'ar

A karo na hudu shugaban Rasha Vladimir Putin wanda ya yi shekaru 18 yana mulkin Rasha ya sake lashe zaben shugaban kasa

Sakamakon farko da kuri’ar jin ra’ayin jama'a a Rasha, sun nuna shugaba Vladmir Putin ya lashe zaben a karo na hudu, da kashi 75 cikin dari.
Kuri’ar jin ra’ayoyin jama’ar ta nuna cewa yana da goyon baya fiye da kowanne daga cikin abokan takararsa, daga masu aikdar kwaminisanci da masu ra'ayin mazan jiya baki daya.
Putin ya kwashe shekaru 18 yana shugabancin Rasha.
Yayi jawabi ga dubban magoya bayansa a dandalin da ake kira Menezhnaya dake kusa da fadar Kremlin a daren jiya Lahadi. Shugaba Putin ya yabawa wadanda suka zabe shi a matasayin "babbar tawaga ko kungiya ta kasa," yace musu "mu tare da nasara."

Da aka tambayeshi ko zai sake tsayawa takara a shekarar 2030, shugaban na Rasha mai shekaru 65 yace wannan ba’a ce, "kana ji zan ci gaba da kasancewa anan har sai na kai shekaru 100 ne?"


Putin ya fafata ne da mutane bakwai, amma babu wani dan takarar da ya zama masa barazana. An yi hasashen sauran yan takarar da suka hada da wani mai gabatar da shirye shiyen telbijin da kuma wani dan kishin kasa basu zasu samu kuru’u masu yawa ba.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG