Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban 'yan tawaye kasar Ukraine, yace ba zasu yi karin shawarwarin samun zaman lafiya ba


Shugaban 'yan tawayen kasar Ukraine Alexander Zakharchenko, a tsakiya kewaye da masu gadi

Wani baban shugaban yan tawaye a gabashin kasar Ukraine, Alexander Zakharchenko wanda yake samun goyon bayan Rasha, yace ba za'a yi karin shawarwarin samun zaman lafiya da gwamnatin kasar ba.

Wani baban shugaban yan tawaye a gabashin kasar Ukraine, Alexander Zakharchenko wanda yake samun goyon bayan Rasha, yace ba za'a yi karin shawarwarin samun zaman lafiya da gwamnatin kasar ba. Ya kuma ce mayanksa suna danawa akan sojojin Ukraine bayan da suka kwace wani filin saukar jiragen sama a ranar Alhamis.
Alexander Zakharchenko shugaban jamhuriyar Donetsk da suka ayyana, yace sojojinsa zasu yi ta kaiwa sojojin gwamnati hari har sai sun kai kan iyakar yankin Donetsk.
Yanzu haka dai yan tawaye ne ke mamaye da muhimman yankunan Donetsk da Luhansk kusa da kan iyakar kasar da Rasha bayan da suka kaddamar da yiwa gwamnatin Ukraine tawaye watani tara da suka shige.
Kafofin yada labarun kasar Rasha sun ambaci Mr Zakharchenko yana fadin cewa babu amfani yin shawarwarin samun zaman lafiya. Ya fadawa kamfanin dilancin labarun Rasha, da ake cewa Interfax cewa tsarin yin shawarwarin samun zaman lafiya da aka yi na'am da shi a Minsk a bara kuskure ne, kuma ba zasu kara yin irin wannan kuskure ba.
Ta wani bangaren kuma, kamfanin dilancin labarun Inerfax ya ambaci wani jami'in yan tawaye mai suna Edurad Basurin yana fadin cewa an kashe fiye da sojojin Ukraine dari bakwai da hamsin a yan kwanakin da suka shige a fafatawar da aka yi na mallakar filin saukar jiragen saman Donetsk, wanda aka lalata.

XS
SM
MD
LG