Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka Zasu Yaki Tsatsauran Ra'ayi A Kasashensu


Wasu shugabannin Afirka a taronsu da suka yi a kasar Mauritania makon jiya

A taronsu da suka kammaa a Mauritania makon jiya shugabannin Afirka sun lashi takobin yaki da tsatsauran ra'ayi a kasashensu da zummar kawar da ta'addanci

Shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka da suka yi taro a Mauritia a makon da ya gabata, sun yi alkawarin kara kaimi wajen yakar kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a nahiyar, musamma ma a yankin Sahel.

Wannan alkwari, na zuwa ne bayan wasu hare-hare da kungiyoyin masu ikrarin jihadi suka kai a wasu kasashen yankin Sahel, ciki har da wani hari da ya halaka sojojin Jamhuriyar Nijar 10 a kudu maso gabashin kasar, da wani hari akan hedkwatar rundunar hadin gwiwar kasashe biyar da ke yaki da masu ikrarin jihadi ta G5 Sahel a Sevare da kuma wasu hare-hare biyu da suka auku a Mali.

Sai dai wasu kwararru sun yi gargadin cewa, da wuya kungiyar ta AU ta iya kara assasa karfi rundunar hadin gwiwar ta G- Sahel, wacce aka kafa a bara.

A wani labari mai nasaba da wannan, wasu mata masu rike da manyan mukamai, sun yi kiran neman karin tallafi daga kasashen duniya, domin taimakawa mata da ‘yan mata su tsira daga matsalolin rikice-rikice da ayyukan ta’addanci da rashin ci gaba da da kasashen yankin Sahel ke fama da su.

Ministar harkokin wajen Sweden, da mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, da wakiliya ta musamman kan harkokin mata, zaman lafiya da tsaro ta kungiyar Tarayyar Afirka ne suka yi wannan kira, bayan da suka kammala wata ziyarar hadin-gwiwa da suka kai Jamhuriyar Nijar da Chadi, inda suka hadu da mata daga bangarorin al’uma daban-daban.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG