Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Duniya Sun Cimma Matsaya Kan Rikicin Libya


Shugabannin kasashen duniya sun amince a jiya Lahadi su mutunta shirin haramta makamai da kuma janyewa daga Libya, inda gwamnatoci masu gaba da juna ke yakin neman shugabanci.

Shugabannin duniya 12 tare da manyan Wakilai daga kungiyoyin Tarayyar Turai da Tarayyar Afrika da Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar kasashen Larabawa sun gudanar da taron kolin wuni guda a birnin Berlin na kasar Jamus.

Mun iya samun amincewar kowa cewa akwai bukatar mutunta yarjejeniyar haramta amfani da makaman a kuma tsaurara aiwatar da wannan matsayar kamar yadda aka yi a baya, inji shugaban Jamus Angela Merkel mai masaukin bakin taron kolin a cikin jawabin ta na karshe.

Ta ce haka batun yake kuma tana ganin abubuwa da suka faru a kwanakin baya sun isa shaidar cewa ayyukan soji ba sune mafita ba, sai dai ya kara jefa mutane cikin wahala.

Mahalarta taron kolin sun amince da yarjejeniyar mako daya na tsagaita wuta a Libya ta kara kaimi. Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterre ya ce akwai bukatar dukkan bangarorin su kara matsin lamba a kan masu gaba da juna a Libya. Ganin cewa kasashen da dama suna marawa bangarori dabam dabam na Libya baya, akwai damuwar cewa Libya ka iya fadawa cikin halin da Syria ta tsinci kanta a ciki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG