Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin kasashen Afirka sun jadada niyar kara hada hannu wajen shawo kan zazzabin malariya


Sauro me kawo cutar zazzabi
Shugabannin kasashen nahiyar Afirka sun bayyana cewa an samu raguwar mace mace ta dalilin kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro da kimanin kashi daya bisa uku cikin shekaru goma da suka shige a nahiyar.

An bayyana haka ne a wani taron manyan kusoshin gwamnati da na cibiyoyin kasashen duniya karkashin shugabancin shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf, wadda kuma take shugabantar kungiyar hadin kan yaki da zazzabin cizon sauro ta shugabannin kasashen Afirka (ALMA), wanda ya sami halartar wakilai da suka hada da shugabannin kasashe da shugaban hukumar hadin kan kasashen nahiyar Afirka, da wakilin babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya da kuma sauraon manyan jami’ai.

Taron ya amince da cewa, koma bayan tattalin arziki da ake fama da shi a kasashen duniya yana kawo koma baya a kokarin cimma burin yaki da cutar a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.

Shugabannin sun kuma bayyana niyarsu ta nuna jagorancin kwarai ta waje amfani da abinda suke da shi a cikin gida yayinda kuma zasu ci gaba da neman hanyoyin samun tallafi daga kasashen duniya. Wannan zai taimaka wajen sa ido kan ci gaban da ake samu a yaki da cutar kanjamau da tarin fuka da kuma zazzabin cizon sauro.

A cikin jawabinsa a wajen taron, darektan yankin na Hukumar Lafiya ta duniya, Dr. Luis Sambo ya bayyana bukatar daukar kwararan matakan da zasu kai ga samun ci gaba cikin sauri a yaki da zazzabin cizon sauro da suka hada da samar da gidajen sauro da aka jika da magani masu karko da yin feshin maganin sauro gida gida da kuma amfani da matakan shawo kan cutar da aka tsara a matakin kasa da kasa.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG