Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kasashen Arewacin Amurka Sun Yi Watsi da Hana Cudanyar Kasuwanci


Shugaban Mexico Enrique Pena Nieto da Firayim Ministan Canada Justin Trudeau da shugaban Amurka Barack Obama

Shugabannin Amurka da Canada da Mexico, da kakkausar lafazi sunyi watsi da guguwar shinge kasuwanni da hana cudanya ta kasuwanni tsakanin kasashen duniya. Shugabannin sun bayyana hakan ne jiya Laraba a wani taron koli da shugabannin kasashen da suke arewacin nahiyar Amurkan suka yi a birnin Ottawa na Canada.

Shugaban Amurka Barack Obama da Firayim Ministan Canada Justin Trudeau, da shugaban Mexico Enrique Pena Nieto, sun yaba da irin nasarori da shirin cinikayya da kasashen uku suka kulla shekaru 22 da suka wuce, da ake kira NAFTA, a dai dai lokacinda ake suka irin wadannan yarjejeniyoyi na kasa da kasa da Amurka da kuma a Turai. Kasashen uku sune suke samar da kashi 27 cikin dari na harkokin kasuwanci a fadin duniya.

'Yan Burundi mazauna Amurka da Canada sunyyi zanga zanga suna kiran shugabannin su taimaka su kubutar da kasarsu daga mulkin kama karya na shugaban kasar
'Yan Burundi mazauna Amurka da Canada sunyyi zanga zanga suna kiran shugabannin su taimaka su kubutar da kasarsu daga mulkin kama karya na shugaban kasar

Da suke amsa tambaya a wani taro da manema labarai da shugabannin duka uku suka yi, kan ko sun damu da irin maganganun da Donald Trump yake yi gameda bakin haure, da shinge kasuwa, Firayim Ministan Canada da shugaban Mexico Pena duk suka ce zasu mutunta duk shawarar da Amurkawa suka yanke kan wanda zai yi musu jagora. Amma duk sun bayyana goyon bayansu kan ci gaba da gudanar d a cinikayya ba tareda tsangwama ba. Haka nan shima shugaban na Amurka ya goyi bayan matsayar da abokan aikin nasa suka dauka kan wannan batu.

Gameda shawarar Ingila na ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai, shugaba Obama yace zai shawarwaci Firayim Minista David Cameron, da shugabar Jamus Angela Markel da sauran shugabanni su nuna dattaku, su gudanar da shawarwari cikin tsanaki.

XS
SM
MD
LG