Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Park Da Kyale Kawarta Ta Kalli Siirin Gwamnati.


Shugabar koriya ta kudu Park Geu hye

Kawar Choi, ba ma'aiakciya r gwamnati bace.

Shugabar Koriya Ta Kudu, Park Geun-hye, tada fada rikicin siyasa kan zargin ta tsoma wata aminiyarta cikin harkokin kasa, alhali ita ba ma'aiakcar gwmanati bacee.
Farin jinita yayi kasa sosai, yayinda ake mata kiraye kirayen tayi murabus, tun bayan da ta bayyana cewa ta bada daftarin jawabanta ga wata aminiyarta mai suna Choi Soon-Sil, ta gyara da bi-biya, alhali bata da izinin kallon sirrin gwamnati. Bayanai sun nuna Choi ta ga wasu bayanan sirrin gwamnati, ciki harda file-file kan kasashen Koriya ta Arewa da kuma Japan.

Park wacce ya rage mata shekara daya da 'yan kai kamin wa'adin mulkinta ya kare, ta nemi jama'ar kasar su gafarceta, duk da haka ta dage cewa zata kammala wa'adinta.

Rahotannin a kafofin yada labaran kasar suna hasashen Choi tayi amfani da kusancinta da shugabar kasar ta shawo kan kamfanoni su bada gudumawa ga kungiyoyin agaji da suek akrkashinta, sannan sai tayi amfani da gudumawar domin wasu muradunta.

XS
SM
MD
LG