Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojin Nigeria sun sami nasarar kame tulin makaman da aka boye a wani rumbun karkashin kasa dake jihar Kano, Nigeria

Hadin gwiwar sojin Nigeria da jami’an ‘yan sandan ciki sun bayyana cewar sun gano wasu damin makamai da aka boye a wani rumbun karkashin kasa a Kebabbun unguwannin Bompai dake Arewa da birnin Kano. Jami’an tsaron suka ce sun kuma gano makaman mallakin kungiyar ‘yan gwagwarmayar Lebanon ce ta “Hezbolla”. Jami’an tsaron na Nigeria, sun nunawa manema labarai tulin makaman da suka gano jiya Alhamis, sannan daga bisani aka sake nuna tulin makaman a gidan Telbijin na Nigeria, wato NTA. Makaman sun hada harda rokokin harba makamai masu linzami da gurneti, da nakiyoyin da ake dasawa a kasa sannan a tadasu suyi barna, da kuma jigidar harsasai da bindigogin hannu.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG