Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Myanmar Zata Gudanar da Bincike Kan Zargin Cin Zarafin 'Yan Rokhingya.

  • Aliyu Imam

Yan gudun hijirar Rokhingya.

Dubban 'yan kabilar ne suke gudun hijira zuwa Bangladesh sakamkon cin zarafin da sojojin kasar suke yi musu.

A Myanmar, jami'an sojojin kasa na kasaer sunce sun fara bincike kan take taken dakarun kasar a jahar Rakhine, inda ake zargin sojojin da aikata munanan cin zarafi babu kyan ji kan tsiraru musulmi na kabilar Rohyingya.

Dubbai sun yi gudun hijira zuwa makwabciyar kasar Bangladesh tun a karshen watan Agusta.

Abunda ba'a sani ba shine lokacinda sojojin zasu bayyana sakamakon bincuken na su.

"Zamu saki rahoton a hukumance, idan muka sami cikakken bayani," kamar yadda wata sanarwar sojojin ta fada.

A yayinda matsalar zamantakewar take kara tsanaini, tsohon babban sakataren MDD Kofi Annan, yana kiran da a kyale 'yan kabliar ta Rohyinga su koma muhallansu

Mr. Annan, wanda a babaya bayan nan ya jgaoranci wani kwamitin MDD kan rikicin na Myanmar, ya fadawa kwamitin sulhu jiya jumma'a cewa "'yan kabilar Rohyinga suna bukatar taimakon su koma muhallansu," ba a tura su sansanonin 'yan gudun hijira ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG