Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SOMALIA: Jiya Laraba Dubban Mutane Sun Gudanar da Zanga zangar Yin Allah Wadai da Harin Mogadishu


Mutanen da suka fito yin zanga zanga

Dubban mutane suka gudanar da zanga zangar yin Allah wadai da harin Mogadishu da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 300 tare da jikata wasu da dama a birnin Mogadishu da wasu biranen kasar Somalia

Dubban mutane sun dunguma akan titunan birnin Mogadishu da kuma wasu manyan biranen Somaliya a jiya Laraba, suna Allah Wadai da wadanda suka kai mummunan harin da ya kashe kusan mutane 300 tare da raunata mutane fiye da 400.

Zanga-zangar da aka yi a birnin Mogadishu na zuwa ne a matsayin mayar da murtani akan kiran da magajin garin Mogadishu yayi, na a gudanar da babban gangami don yiwa wadanda aka kashe da wadanda suka jikkata a harin bam na mota da aka kai ranar Asabar din da ta gabata addu’o’i, wanda gwamnatin kasar ta dora laifin akan ‘yan kungiyar al-Shabab.

Gabanin gangamin, wasu matasa maza sanye da jan rawani sun tilastawa masu sana’o’i rufe guraren sana’arsu.

Masu zanga zangar, da suka yi ta fadin “Allah wadan makiya, Allah wadan ‘yan kungiyar al-Shabab” da karfi, daga baya kuma suka taru a filin wasan kwallon kafa na birnin Banadir, inda shugaban kasar da wasu jami’ansa suka hadu da su.

Shugaban kasar ta Somalia, Mohammed Abdullahi Mohamed yayi kira ga ‘yan kasar da su yi shirin abin da ya kira yaki da kungiyar al-Shababa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG