Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tabarbarewar Tattalin Arzikin Iran Ya Tilastawa 'Yan Kasar Shiga Zanga-zanga


'Yan Iran dake zanga zanga akan tabarbarewar tattalin arzikin kasarsu

Daruruwan 'yan kasar Iran suka shiga gangamin kin amincewa da munancewar tabarbarewar tattalin arzikin kasar da ya jefa rayuwarsu cikin mawuyacin hali

Daruruwan yan kasar Iran ne suka shiga ganganmin akan titunan a birnin Tehran domin nuna rashin amincewa akan munancewar tabarbarewar tattalin arzikin kasar, matakin daya zama zanga zanga mafi girma na kin jinni manufofin gwamnatin kasar, rabon da aga irin haka anyi shekaru.

An faro zanga zangar ta jiya Litinin ce daga wurin da ake kira Grand Bazaar, inda kafofin yada labarun kasar da shedun gani da ido suka ce masu shago sun rufe kantunan su domin nuna fushin su ga rashin kasuwa da kuma yadda darajar takardun kudin kasar ke faduwa, da suka yi faduwar kashi hamsin daga cikin dari cikin watani shidda da suka shige.

Hotunan vidiyo da sashen Persha na nan muryar Amurka ya samu daga mutanen yankin sun nuna daruruwan masu shago da wasu masu zanga zanga suna wucewa ta titunan tsakiyar birnin Tehran suna kururuta la’anar manufofin gwamnatin kasar.

Facebook Forum

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG