Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tagwayen Bama Bamai Sun Hallaka Mutane 8 Da Jikkata Wasu Da Dama A Turkiyya


Jami'ai a kasar Turkiyya sunce mutane 8 ne suka mutu sakamakon tagwayen harin da ‘yan tawayen kurdawa dake kudu maso gabashin kasar suka kasar suka kai, haka kuma mutane da dama sun samu rauni.

‘Yan tawayen na jamiyyar Ma'aikata da ake kira Kurdistan Workers Party ko kuma PKK a takaice sun tada bomb ne a gefen hanya a garin Kiziltepe, dake yankin gundumar Mardin inda hakan yayi dalilin mutuwar mutane 3 nan take kana wasu 25 suka samu rauni daban-daban, cikin wadanda suka jikatta ko har da yara kanana su 5.

Haka kuma wata mota dauke da boma-bomai tayi bindiga da niyyar auna ‘yan sanda a wani bangaren sanannen birnin tarihin nan na Diyarbakir, kuma hakan yayi dalilin mutuwarr mutane 5 fararen hula kana wasu 12 sun samu rauni daban-daban

Duka boma-boman da aka tayar an tada su ne da niyyar kaiwa ‘yan sanda hari amma kuma sai ya fada kan fararen hula.

Wannan harin bomb din yazo ne ‘yan saoi kadan bayan an danganta laifin kashe wasu sojoji 4 tare da jima wasu 9 rauni ga kungiyar ta PKK, wannan abu dai ya faru ne a kusa da bakin iyakar kasar Iraqi.

Sakataren tsaron Amurka Ash Carter ya aika wa kasar ta tukiyya da sakon jaje da kuma wadanda wannan lamari ya rutsa dasu, kana ya bayyana goyon bayan Amurka na hada hannu da kasar ta Turkiyya domin yaki da yan taaadda.Duka kasashen biyu dai suna kallon kungiyar PKK a matsayin na ‘yan ta'adda.

XS
SM
MD
LG