Shugabannin kungiyar tarayyar turai sun kammala wani taron koli na musamman da suka yi a Brussels,inda suka aikewa Britaniya sako palo-palo, cewa kada ta ja jiki wajen daukan matakan ficewa daga kungiyar kuma kada tayi tsammanin wani sassauci, amma ta yi tsaye wajen ganin ta yunkura a fita daga shirin tarayyar turan d a bashi da farin jini.
"Akwai mutane da dama, wadanda basa jin dadin hali da ake ciki ahalin yanzu, kuma suna son ganin mun inganta ayyukanmu, inji shugaban majalisar Turan, Donald Tusk yayin taron manema labarai a babban birnin kasar Belgium din jiya Laraba. Ya kara da cewa shugabannin zasu sake zama cikin watan Satumba domin shawarwari kan matakai da zasu dauka bayan ficewar Ingila daga kungiyar.
Taron na kwanaki biyu ba'a taba irinsa ba, saboda kasashen sun maida hankali kan abunda ya biyo bayan kuri'ar da Ingila ta kada, da faduwar hannayen jari a kasuwnanin duniya, matakin da ya janyo tunani mai zurfi kan yadda za’a yiwa kungiyar mai kasashe 28 garambawul.