Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarzoma ta barke tsakanin Israila da Falasdinawa kusa da kogin Jordan


Jami'an Israila suna kawar da gawar Falasdinu da suka harbe

Jiya Alhamis aka sake samun barkewar wata tarzoma tsakanin Israila da Falasdinawa da tayi sanadiyar mutuwar Falasdinawa hudu

Wata sabuwar tarzoma ta barke a yammacin kogin Jordan a jiya Alhamis, har jami'an tsaron Isra'ila suka harbe suka kashe Falasdinawa uku wadnada suka kai hare hare da wukake da kuma farwa mutane da mota, mutum na hudu an kashe shi ne a wata arangama da dakarun Isra'ila.

A harin farko, wani Bafalasdine ya dabawa wasu masu aikin gadi ko tsaro su biyu wuka a a yammacin kogin Jordan a garin da ake kira Ariel, kamin a harbe a kashe su.Jim kadan bayan wannan ne wani Bafalasdine yayi kokarin ya kaiwa sojojin Isra'ila hari da da irin abun kunce daurin karfe kusa da garin Hebron amma sun harbe suka kashe shi. An harbe aka kashe wani Bafalasdine bayan da yayi kokarin ya farwa wani soja da mota.

Sojojin Isra'ila sun kashe wani bafalasdine na hudu, a yayinda suke kokarin kama wani kusa da garin Qalandiya a yammacin kogin jordan.

Wannan tarzomar tana zuwa ne a dai dai lokacinda a cikin watannin baya bayan nan, hare haren da Falasdinawa suke kaiwa kan Yahudawa ya assasa, ita kuma Isra'ila take daukar matakan kare jama'arta, wanda babu alamar sassautawa.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG