Accessibility links

Tawagar Muslmai Da Krista Ta Yi Bude Baki Da Sultan


Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar

Wata tawagar matsan krista ta kaiwa Sultan na Sokoto ziyara inda ta yi bude baki da shi

Sau da yawa masana a Najeriya na cewa yawancin tashin hakali a kasar basu da nasaba da addini to amma kuma an fi fakewa da addinin a aikata ta'asa musamman a arewacin kasar. Sabili da haka ne kungiyoyi masu neman zaman lafiya suka tashi haikan su shawo kan lamarin.

Daya daga cikin kungiyoyin neman zaman lafiya tsakanin Musulmai da Kristoci a Najeriya ta nada wata tawaga da ta kunshi Musulmai da Kristoci da ta kai ziyarar ban girma da bude baki a watan azumi mai alfarma ga Maimartaba Sarkin Musulmi Alhaji Mohammad Sa'ad Abubakar a Sokoto. Bayan bude bakin jawaban sanatarwa ne suka biyo bayan bude bakin musamman ga shugabannin da matasa dangane da hanyoyin tabbatar da zaman lafiya a Najeriya. Fasto Yahana Waidi Buru shi ne shugaban kungiyar. A jawabinsa faston ya ce a rayuwarsa bai taba tunanen zai taba zama da Sultan har su yi bude baki ba. Ya ce duk mai imani zai mutunta addinin kowa. Ya ce tunda Kristoci da Musulmai suna Najeriya to dole ne su zauna da juna cikin lumana da kwanciyar hankali.

Shi kuma dan rajin kare hakin bil adama Barista Solomon Dalung wanda ya jagoranci tawagar yana ganin irin wannan ziyarar ita ce zata kawo zaman lafiyar da aka rasa a kasar. Ya ce da zara babu zumunci tsakanin mutane to kiyayya zata shigo. Zumunci ne kawai ka iya gina soyayya tsakanin Musulmai da Kristoci a Najeriya.

Da yake jawabi Sarkin Musulmi ya ce wannan aikin da matasan suke yi kalubale ne ga manya magabata. Ya ce kamata ya yi a ce su magabata ne ke yin irin wannan aikin. Ya ce ga 'ya'yanmu da jikokinmu na kokarin samu a hanya maimakon mu sa su. Yayin da magabata ke cusa kiyayya da gaba a cikin jama'a su kuma matasa suna neman hadin kai ne.

Daga karshe Maimartaba ya ce duk inda gaskiya da adalci suke nan ne suka sa gaba.

Ga karin bayani daga Murtala Faruk Sanyinna.

XS
SM
MD
LG