Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Ma'aikata Ceto Na Ci Gaba Da Zakulo Mutane A Mexico


A yau alhamis tawagar Ma’aikatyan ceto a Mexico ta yi kokrin kaiwa ga wadanda suka makale a cikin gine ginen da suka rushe a lokacin mummunar girgizar kasa data hallaka sama da mutane 230.

Daya daga cikin binciken da aka gudanar a birnin Mexico, an yi shi ne a wata makaranta wanda a ranar laraba ma’aikatan suka hango wata yarinya da tarkace ya bizne ta kuma sun iya gane cewa tana raye ta hanyar fada mata ta motsa hannun ta.

An gudanar da wannan bincike daga daren laraba harzuwa safiyar alhamis tare da kiyayewa dan kaucewa rugujewar tarin baraguzai yayin da suke kokarin kaiwa gareta.

Rodolfo Ruvalcava, daya daga cikin ma’aikatan coton ya fadawa kafar talabijin ta FORO TV cewar “Yarinyar ta fada mana sunanta Frida, kuma bayan haka ta fada mana cewa akwai sauran yara biyu, da kuma sauran mutane amma bamu sani ko sauran suna raye ba.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG