Accessibility links

Ted Cruz Yayi Amai Ya Lashe Game Da 'Yan Najeriya


Sanata Ted Cruz, dan bangaren masu tsananin ra'ayin rikau na jam'iyyar Republican ta Amurka.

Dan majalisar dattijan mai tsananin ra'ayin rikau ya nemi gafarar kalamunsa na cewa shugaba Obama ya dauki 'yan damfarar Najeriya su gudanar da shirinsa na kiwon lafiya

Dan majalisar dattijan Amurka Ted Cruz, ya nemi gafarar 'yan Najeriya game da kalamun da yayi cewa shugaba Barack Obama ya dauko 'yan damfarar Najeriya domin su gudanar da dandalin intanet na shirinsa na fadada kiwon lafiya, Obamacare, shi yasa dandalin ya kasa aiki.

Sanata Cruz, dan bangaren nan da ake kira Tea Party na masu matsanancin ra'ayin rikau na jam'iyyar Republican, ya fada a wani gangamin siyasar da yayi a jiharsa ta Texas cewa yanzu ba a jin duriyar 'yan damfarar nan na Najeriya a saboda duk "Obama ya kwashe su ya ba su aiki."

Wannan kalami nasa ya harzuka 'yan Najeriya dake zaune a nan Amurka, inda har jakadan Najeriya ma ya rubuta takarda mai zafi ga sanatan kan wannan kalami nasa.

Sanata Cruz ya bayarda takardar neman ahuwa yana mai cewa ya fadi wannan kalami ne cikin raha ba don ya bakanta ma 'yan Najeriya ba, har ma yace matarsa ma tana da alaka da Najeriya domin ta zauna a kasar tare da iyayenta da suka tafi aikin mishan.

Haka kuma, Sanata Cruz ya nemi ganawa da jami'an kungiyoyin 'yan Najeriya da na ofishin jakadancin Najeriya domin ya rarrashe su tare da neman gafararsu ido da ido.

Shugababn sashen Hausa na Muryar Amurka, Leo Keyen, da Ibrahim Garba sun tattauna kan wannan batu na kalamun Ted Cruz da neman gafarar da yayi.

XS
SM
MD
LG