Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohuwar Ministar Mata Aisha Jummai Alhassan Ta Rasu


Hajiya Aisha Jummai Alhassan (Twitter/ Aisha Jummai)
Hajiya Aisha Jummai Alhassan (Twitter/ Aisha Jummai)

Tsohuwar ministar wacce ake wa lakabi da “Mama Taraba” ta rasu ne a wani asibiti a birnin Alkahira na kasar Masar a cewar Ango.

Rahotanni daga jihar Tarabar Najeriya na cewa tsohuwar ministar mata Hajiya Aisha Jummai Alhassan ta rasu. Shekarunta 61.

Sadiq Ango, da ga marigayiya, ya tabbatarwa da Muryar Amurka rasuwar mahaifiyar tasa.

Tsohuwar ministar wacce ake wa lakabi da “Mama Taraba” ta rasu ne a wani asibiti a birnin Alkahira na kasar Masar a cewar Ango.

A shekarar 2015, Alhassan ta yi takarar gwamnan jihar Taraba karkashin tutar jam’iyyar APC mai mulki, amma ta sha kaye a hannun Gwamna mai ci Darius Ishaku na jam’iyyar PDP.

Ta kuma sake yin takarar kujerar a shekarar 2019 karkashin jam’iyyar UDP. amma gabanin hakan, bayan da ta fadi a zaben 2015, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada ta mukamin ministar mata.

Karin bayani akan: PDP, APC, Shugaba Muhammadu Buhari, Muryar Amurka, Nigeria, da Najeriya.

A shekarar 2010 Mama Taraba, ta shiga harkar siyasa, inda ta fara da neman takarar kujerar sanata karkashin jam’iyyar PDP.

Ta kuma lashe zaben, inda ta ka da tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame wanda ya yi takara karkashin jam’iyyar ACN.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG