Accessibility links

Tsohon gwamnan Yobe ya zargi shugabannin Najeriya da nuna fifiko ma wasu sassa na arewa kan arewa maso gabashin kasar.

Tsohon gwamnan Yobe Sanato Abubakar Ibrahim ya zargi shugabannin kasar da nuna wa wasu sassan arewa fifiko fiye da arewa maso gabashin kasar.

Sanato Abubakar Ibrahim ya ce tun mutuwar Sir Abubakar Tafawa Balewa a shekarar 1966 shugabannin Najeriya wadanda yawancinsu sun fito ne daga arewa maso yammacin kasar suka mayarda arewa maso gabashin kasar saniyar ware. Ana ta nuna ma arewa maso yammaci da wasu sassan Najeriya fifiko bisa ga arewa maso gabashi. Ya ce ana yiwa shiyar kashin dankali da musgunawa da zagen danwake da ya ce al'ummar shiyar ke fama da shi. Ya ce duk wadanda suka yi shugabancin Najeriya babu wanda ya yi abun a zo a gani a arewa maso gabashin kasar. Ya ce kodayake su ne kashi talatin cikin dari na al'umar kasar amma kullum suna baya ko ana batun ilimi. hanyoyi ko sauran abun moriyar rayuwa.

Game da ayyukan gwamnatin tarayya a yakin na nera biliyan 90 ne kawai a duk jihohin shida. Ya ce kuma sai jihohin kudu maso gabashin kasar da suke da ayyuka na nera biliyan 160. Kudu maso yamma nada ayyukan nera biliyan 1300 da 'yan kai.Arewa maso yamma nada nera biliyan 500 kana arewa ta tsakiya nada nera biliyan 700. Ba'a ma batun uwa uba jihohin kudu masu kudu.

Ya ce wannan shugaba mai ci yanzu shi ma ya cigaba da yin hakan domin abun da ya tarar a kasa ke nan.

Ibrahim Abduaziz nada rahoto.

XS
SM
MD
LG