Accessibility links

Tsugune Bata Karewa Majalisar Niger Ba


Mr. Morou Amadou, ministan shari'a na Jamhuriyar Niger.

Da alama takaddama da majalisar dokokin jamhuriyar Niger ta shiga lamarin da ya tilasta mata ta je hutun dole bai kare ba.

Bisa ga duka alamu takaddamar da ta kunno kai a kajalisar dokokin jamhuriyar Niger tana nan kasa tana kara ruruwa.

Kafin su tafi hutun dole sun kwashe makonni daya suna ta kai ruwa rana akan takaddamar da ta kunno kai a majalisar dokokin kasar. Takaddamar tana da alaka da batun nadin mukamai biyu daga cikin mukamai goma sha uku.

Barkewar rigimar ta sa shugaban majalisar dokokin kasar ya dakatar da ayyukan majalisar domin samun shawarar kotun koli akan lamarin. Ranar juma'a da ta gabata kotun ta warware sarkakiyar da majalisar ta samu kanta ciki. Kotun ta gyara masu zama akan rudanin da suka shiga.

Dan majalisar Zakari Umaru daga jam'iyyar PNDS mai mulki yace suna nan akan bakarsu na cewa duk abun da masu gayon bayan shugaban kasa suka ce shi zasu yi. Yace takaddama ta kare sai dai wanda yayi niyar taka dokar da kotu ta tsayar.

To saidai bangaren adawa sun kuduri aniyar ture shawarar kotun kasar. Tijani Abdukadiri dan majalisa bangaren adawa yace an yita ta kare. Yace su basu ware kowa ba amma 'yan bangaren adawa dake goyon bayan gwamnati su ne suka ware kansu. Yace suna son kotu ta bayyana wa duniya idan dan majalisa yana cikin adawa kuma a ce yana cikin gwamnati mai ci.

Yau majalisar zata sake komawa zama yayin da gwamnati ta sauya masu tsaron shugaban majalisar. Amma shugaban majalisar Hamma Ahmadu yace yaki ya amince da sabbin jami'an dake tsaronsa. Wannan wani sabon babi ne na rikici aka bude.

Ga rahoton Abdullahi Maman Ahmadu
XS
SM
MD
LG