Accessibility links

Turkiya ta Harbo Jirgin Syria


TURKIYA TA HARBO JIRGIN SYRIA

Turkiyya ta harbe wani jirgin yakin Syria lokacin wani kazamin artabu tsakanin sojojin Syria da ‘yan tawaye kasar kusa da kan iyakar kasashen biyu.
PM Turkiyya Recep Tayyib Erdogan yace jirgin saman yakin Syrian ya shiga sararin samaniyar Turkiyya. Tashar talabijin ta Syria tace jirgin yana bin ‘yan tawaye ne cikin hurumin sham watau Syria.
Wata majiya ta sojojin Syria tace matukin jirgin ya samu sukunin fita daga cikin jirgin. Wani kakakin sojan Syria ya kira matakin da turkiyya ta dauka “a matsayin cin zali a zahiri”.
Mr. Erdogan ya gargadi Syria cewa “martanin da kasarsa zata dauka zai kasance mai tsanani, muddin ta keta sararin samanaiyar kasarsa”.
Cikin kwanaki uku da suka wuce ‘yan tawayen Syria da sojojin gwamnatin kasar suna fafatawa domin iko kan garin kasab na tsallake dake kan iyakokin kasashen biyu a lardin Latakia.
Ahalinda ake ciki kuma PM Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, yayi watsi da zarginda ake yi masa cewa baya da jumurin sauraron ra’yoyin siyasa da suka saba nasa, dalilinda yasa ya haramta ko ya bada umarnin dakile dandalin twitter cikin kasar.
A wani gangamin siyasa da ya gudanar jiya lahadi, Mr. Erdogan ya tabbatar da cewa ya bada umarnin a rufe dandalin Twitter a Turkiyya.
XS
SM
MD
LG