Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiya Ta Soki Amurka Kan Janyewa Daga Yarjejeniyar Nukiliyar Iran


Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan

Yayinda yake nuna goyon bayanshi ga kasar Iran shugaban Turkiya ya soki shugaban Amurka da kakkausan lafazi saboda yanjewa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran

Kasar Turkiyya ta soki shugaban Amurka Donald Trumpda kakkausar lafazi kan shawarar daya yanke na janyewa daga yarjejeniya da aka cimmawa da kasar Iran game da shirin ta na nukiliya.

Shugaban na Turkiyya Racep Tayip Erdowan yayi gargadi akan irin mummunar abinda ka iya biyo bayan janyewar da Amurka tayi daga cikin wannan batu.Tare da masu kula da al’amurran da kanje su komo na cewa Turkiyya na iya samun kanta shiga cikin wani sabon rikicin da ka iya barkewa tsakanin Amurka da Iran din.

Erdowan ya tattauna ta wayan tarho da takwaran aikin sa na Iran Hassan Rouhani a ranar Laraba.

Majiya daga fadar shugaba kasar na Turkiyya na cewa Erdowan ya jaddada goyon bayan sa ne game da wannan yarjejeniyar nukiliyar da aka cimmawa da kasar ta Iran kana yana sukan shawarar da Trump ya dauka akan wannan lamari.

Yanzu haka da Turkiyya na daukar dawainiyar ‘yan gudun hijirar Syria har su miliyan 3 kuma fatar ta shine ganin an kawo karshen fadan da ya rabo su da muhallan su domin su koma gida.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG