Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

VOA Hausa Da Freedom Radio Zasu Dauki Muhawara Kan Ilmi Yau Jumma'a


VOA Hausa Da Freedom Radio Zasu Dauki Muhawara Kan Ilmi Yau Jumma'a

Masu sauraro su na iya kira da karfe 5 na maraicen yau jumma'a domin shiga cikin wannan muhawara da 'yan takarar manyan jam'iyyu a Kano

A yau jumma'a da karfe 5 Sashen Hausa na Muryar Amurka tare da gidan rediyon Freedom FM dake Kano a arewacin Najeriya zasu gudanar da muhawara ta hadin guiwa kan batun bunkasa ilmi a tsakanin 'yan takarar manyan jam'iyyu a Jihar Kano.

Dukkan manyan jam'iyyun, watau ANPP mai mulki, da PDP, da CPC, da ACN sun yarda zasu turo wadanda za su bayyana shirye-shiryensu na bunkasa ilmi a Jihar idan har aka zabe su.

Masu sauraro zasu iya shiga cikin wannan muhawara ta hanyar bayyana a dakin shirye-shirye na gidan Rediyon Freedom a Kano, ko kuma ta kira kai tsaye zuwa nan Washington a kan wadannan lambobi:

+12026190154 ko kuma +12026190155

Wannan muhawara dai zata ta'allaka ne kan hanyoyin magance matsalolin da suke fuskantar ilmi, musamman a jihar Kano da kuma jihohin arewacin Najeriya inda aka samu koma-baya sosai cikin 'yan shekarun nan a fagen ilmi.

XS
SM
MD
LG