Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wanda Ya Jefi George Bush Karami Da Takalma A Iraqi Yana Takarar Kujerar Majalisa.


Muntadhar al-Zeidi, a tsakiya a wata unguwa yayinda yake yakin neman zabe.

Dan jaridar da yayi fice a 2008 saboda jifar shugaban Amurka a lokacin George Bush da takalama, yana takarar kujerar majalisar dokokin kasar a zaben da za'a yi ranar 12 ga watan nan.

A Iraqi, dan jaridar kasar da ayi suna a 2008 saboda jifar shugaban Amurka George Bush da yayi da takalman sa, ya shiga siyasa harma yana takara.

Da yake magana da manema labarai a jiya Jumma'a lokacin da yake yakin neman zabe kujera a majalisar dokokin kasar, Muntadhar al-Zeidi, yace yana son Amurka ta nemi gafara saboda yaki data kaiwa kasar ta Iraqi, kuma ta biya diyya ga iyalan da yaki ya rutsa da sauran wadanda lamarin ya shafa.

A shafin yakin neman zabensa a dandalin Face book, akwai fefen vidiyon lokacinda yake wurgin shugaban na Amurka da takalama.

Daga bisani ne jami'an tsaro suka tasamma masa, aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 3 a gidan yari, yayi zaman sarka na watanni tara, daga nan sai ya koma birnin Beiruit a Lebanon, da kuma turai. Kodashke sai a kwananan ya koma kasar su, jifar shugaban na Amurka yasa ya sami sanuwa a kasar su ta Iraqi, da kuma a aduk fadin kasashen larabawa.

An tsaida 12 ga watan nan ranar zabe a Iraqi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG