Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Magani Zai Dinga Tantance Cikin Mutum Yana Aikawa Likitoci Sako Akan Cututtuka


Sabon maganin

Idan mutum ya sha wannan sabon magani da aka kirkiro zai dinga aikawa likitoci rahoto akan kowace irin cuta take cikin mutum lamarin da zai taimaka a dauki matakin gaggawa

Kwanan nan wani sabon magani da aka kirkiro zai rika aikawa da sako daga cikin mutum zuwa ga likitoci ta yadda zai taimaka masu wajen tantance cututtuka kama daga olsa zuwa kansa zuwa sauran kumburi da dai sauransu a cewar wani sabon nazari.

Masana ilimin kimiyya sun kirkiro wani dan karamin kabso mai kunshe da garwayen kofin sinadarin halitta da kuma lataroni wanda zai iya gano duk inda jini ke yoyo a cikin mutum.

Za a iya amfani da wannan kabso din a fannin asibiti da muhalli da dai sauran fannoni, bisa ga nazarin.

Fannin kofin sinadarin halittan da ke cikin kabso din na kunshe da wata kwayar halitta ko bacteria da Turanci, wadda kan yi haske idan ta rabu da garwayen jini.

Fannin lataroni na kabso din ya kunshi wani karamin abin gano haske, da wata 'yar karamar komfuta, da batiri da na'urar tura sako mai tura bayani zuwa wayar salula ko kuma komfuta a waje.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG