Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

WASHINGTON DC: Taron Addu'o'i wa Jakadan Najeriya da Ya Rasu


Jiya Alhamis aka yi taron addu'o'i ma jakadan Najeriya a Amurka wanda ya rasu makon jiya.

An rera wakoki a taron addu'o'in na musamman saboda tunawa da jakadan Najeriya wanda Allah ya karbi ransa makon jiya.

An shirya taron ne a ofishin jakadancin Najeriya dake tsakiyar birnin Washington DC fadar gwamnatin Amurka domin yin bankwana da karrama Jakadan Najeriya a Amurka Farfasa Adebowale Adefoye.

Jakadan ya rasu ne a ranar 27 ga watan Agustan wannan shekarar.

Da yawa daga cikin wadanda suka halarci taron akasarinsu suna sanye da bakin kaya ne sun zub da hawaye yayinda ake gabatar da jawabai masu sosa rai da suka ta'allaka akan halayen marigayin.Haka ma aka tuna da irin gudummawar da ya dinga bayarwa tun yana malamin jami'a.

Da shiga dakin taron abun da mutum zai fara kicibar dashi shi ne wani babban hoton marigayin wanda aka dauka yana murmushi a lokacin da yake raye..

Mai lura da ofshin jakadancin Najeriya a yanzu Hakim Balogun shi ya fara gabatar da nashi takaitaccen jawabin. Yace zuciyarsa na cike da jimame da bakin ciki wanda ni kadai ke jinshi. "Allah ya riga ya yi zabinsa na daukan ran maigidanmu, shugabanmu, malaminmu kuma abokin aikinmu"-inji Balogun.

A nashi tsokacin shugaban kungiyar jakadojin kasashen nahiyar Afirka a birnin Washington DC jakadan kasar Saliyo Mr. Bukari Stevens ya bayyana Farfasa Adefoye a matsayin wanda ya kare muradun Najeriya da ma Afirka.

Yace marigayi Farfsa Adefoye mutum ne mai basira da ilimi kuma ya cancanci matsayin da ya bautawa kasarsa. Mutum ne kuma da ya tashi haikan ya kare kasarsa da Afirka.

Mataimakiyar skataren harkokin wajen Amurka dake lura da harkokin Afirka Linda Thomas Greenfield cewa ta yi "ba zan boye maku ba. Na yi matukar bakin ciki da wannan rashi"

Miss Olufunmi Adefoye na daya daga cikin 'ya'yan marigayin. Tayi jawabi mai sosa rai wanda ya sa mutane da dama suka yi hawaye. Tace da ikon Allah sun sami karfin gwiwar jimre rashin da suka yi.

Dr Hassana Halidu jakadiyar Jamhuriyar Nijar ta halarci taron.Tace cikakken jakada ne wanda ya sa Najeriya da Afirka a ransa.

Shi ma mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya ya ce yayi anfani da mukaminsa wurin yiwa kasarsa kokari matuka.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

XS
SM
MD
LG