Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Kasashen Waje Na Kokarin Leken Asirin 'Yan Takarar Shugabancin Amurka


James Clapper, daraktan hukumar leken asiri ta Amurka
James Clapper, daraktan hukumar leken asiri ta Amurka

Yayinda yake jawabi James Clapper ya jawo hankalin 'yan jami'a, tsaro akan wasu kasashen duniya dake kokarin leken asirin 'yan takaran neman shugabancin Amurka a zaben bana

Manyan jami'an leken asiri na gwamnatin Amurka sunce akwai alamun masu satar shiga yanar gizo daga wasu kasashen waje suna kokarin leken asirin 'yan takaran shugabancin Amurka.

Daraktan hukumar leken asirin Amurka James Clapper yace akwai kwakwaran alamun hakan .

Jiya Laraba Mr. Clapper ya yi wannan furuci wajen wani taro da aka yi akan matakan tsaron hanyoyin sadarwa.

Yace tuni jamai'an daga hukumar binciken aikata manyan laifuka ta FBI da ma'aikatar tsaron cikin gida suke yin aiki tare da ofishin yakin neman zabe domin dakile duk wata barazanar satar bayanansu daga yanar gizo.

Wannan zato ba zai rasa alaka da abubuwan da suka faru ba a lokacin yakin neman zabe guda biyu na baya. Jami'an leken asirin Amurka sun ce satar shiga kafofin yanar gizo ya zama ruwan dare gama gari a shekarar 2008 inda suka auna Shugaba Obama da abokin hamayyarsa Miitt Romney.

XS
SM
MD
LG