Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Manyan Jami'an Amurka Sun Ce Korea ta Arewa Na Iya Kai Hari Kan Amurka cikin 'Yan Watanni Masu Zuwa


H. R. McMaster da Mike Pompeo

Daraktan hukumar leken asiri, CIA, Mike Pompeo da Janar McMaster mai ba shugaban Amurka shawara dangane da harkokin tsaro sun fada jiya Alhamis Korea ta Arewa na iya kai hari da makaman nukiliya kan Amurka cikin 'yan watanni masu zuwa

Wasu manyan jami’an Amurka guda biyu sun ce akwai yiwuwar Korea ta Arewa ta iya kawo harin makaman nukiliya akan Amurka nan da wasu ‘yan watanni masu zuwa.

A jiya Alhamis, Darektan hukumar leken asirin kasar ta CIA, Mike Pompeo ya fadawa wani taro a nan Washington cewa “yana cikin matukar damuwa” kan yadda Korea ta Arewa ke kara zafafa barazanarta da kuma yiwuwar ta haifar da gwagwarmayar neman mallakar makaman nukiliya a tsakanin kasashen dake yankin gabashin Asiya.

“Ya kamata mu rika dauka tamkar sun cimma wannan buri na su ne,” in ji Pompeo a lokacin da aka tambaye shi kan yiwuwar Pyongyang ta kawo hari akan wasu muhimman wurare a cikin Amurka.

“Tuni sun riga sun yi nisa wajen cimma wannan burin, yanzu an kai wurintunanin: ta yaya za a iya ja musu burki?”

Bayan haka ne kuma, a ranar ta Alhamis, mai ba da shawara kan harkar tsaro Janar H.R McMaster, ya ce hukumomin Washington na fadi-tashin ganin an shawo kan wannan lamari ba tareda an kai ga daukan matakin soji ba.

H. R. McMaster
H. R. McMaster

Wadannan kalamai na Pompeo da McMaster na zuwa ne yayin da ta da jijiyar wuyan da ake yi tsakanin Amurka da Korea ta Arewa ke ci gaba da zafafa, bayan gwajin makamin nukiliya na baya-baya nan da Pyongyang ta yi a watan da ya gabata, wanda shi ne na shida a jumullance, da gwaje-gwajen da ta sha maimaitawa na makaman da jami’an leken asiri suka ce sun hada da makaman linzami masu tafiyar matsakaici da dogon zango.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG