Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu sun harba roka a wata matatar tace iskar gas a Algeria


Matatar iskar gas a Algeria

Wasu mahara da ba a san ko su waye ba, sun harba roka a wata matatar tace iskar gas da ke kudancin Algeria a yau Juma’a, sai dai babu rahotan da ya nuna cewa an samu jikkata.

An harba rokar ne da misalin karfe 6 na safe a gogon yankin a ma’aikatar, wacce ke karkashin kulawar wasu kamfanoni uku, cikinsu har da wani kamfanin kasar Norway da ake kira Statoil.

Wata sanarwa da kamfanin na Statoil ya fitar, ta nuna cewa harin ya kaikaici matatar iskar gas da ake kira In-Salah da ke yankin Krechba.

Rahotanni sun ce ma’aikata uku da ke aiki a kamfanin suna cikin koshin lafiya, kuma babu wani rahoto da ya nuna cewa wani ya samu rauni.

Kamfanin BP na Burtaniya da ke da hanun jari a kamfanin, ya ce tuni an rufe ma’aikatar saboda kare lafiyar ma’aikata.

A watan Janairun shekarar 2013, wasu mayakan Islama sun taba kai hari a kamfanin matatar gas na Amenas da ke gabashin Algeria, inda aka yi garkuwa da mutane 40 wadanda mafi yawansu ‘yan kasashen waje ne, har wasunsu ma suka mutu.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG