Accessibility links

Wata kotu a Maiduguri ta samu wata mace da laifin kasa da gangan kuma tayi mata hukuncin kisa ta hanyar ratayewa.

Wata mace 'yar shekara ashirin da biyar da wata kotu a Maiduguri tace ta kashe wasu yara da gangan ta samu hukuncin kisa ta hanyar ratayewa.

Alkalin Kotun Justice Wakil Gana yace kotun ta samu matar Hauwa Ayuba da laifin kashe wasu yara biyu da gangan wato Aishatu Nuhu 'yar shekara shida da haihuwa da Abubakar Nuhu dan shekara goma da haihuwa wadanda ta ba abun sha dake da guba. Ta ba babbar 'yar dake da shekara goma sha biyu da haihuwa Fatima wadda ta tsallake rijiya da baya.

Hauwa Ayuba ta kuma dauki wuka ta yanke zakarin wani yaro dan shekaru hudu da haifuwa. Ta kuma sassare mahaifiyar yaran da adda mai suna Aishatu Nuhu.

Wadannan abubuwan al'ajabi sun faru ne a garin Gwandali kusa da Maiduguri kimanin watanni shida da suka gabata.

Alkalin kotun yace duk da abubuwan da Hauwa Ayuba tayi bata nuna nadama ba. Yace kafin kotun ta zartas da hukuncin sai da tayi bincike akan matar a tabbatar bata da tabun hankali. Yace amma tana da damar daukaka kara. Da matar ta ji hukuncin sai ta fashe da kuka tana ambatar sunan wasu da tace sun kwareta.

Duk wadanda Hauwa ta kashe da kuma ta raunata iyalan mutum guda ne wato Nuhu Gwandali wanda kuma wa ne ga mijin ita Hauwa. Malam Nuhu Gwandali yace uwarsu daya ubansu daya da mijinta domin haka abun yayi masa ciwo.

Ga karin bayani.
XS
SM
MD
LG