Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yada kwayar cutar kanjamau daga uwa zuwa jariri ya ragu a Afrika ta Kudu


Wata mace da danta a dakin jinya

Jami’an aikin jinya na kasar Afrika ta Kudu sun ce wani sabon shiri da ake aiwatarwa da nufin hana jariri daukar da cutar kanjamau daga uwarshi ya taimaka wajen hana dubabban jarirai kamuwar da kwayar cutar.

Jami’an aikin jinya na kasar Afrika ta Kudu sun ce wani sabon shiri da ake aiwatarwa da nufin hana jariri daukar da cutar kanjamau daga mahaifiyarshi ya taimaka wajen hana dubabban jarirai kamuwar da kwayar cutar. Hukumar binciken kwakwa ta Afrika ta Kudu tace sakamakon binciken da aka fitar a taron kanjamau da aka gudanar a Durban na shekara ta dubu biyu da goma sha daya na nuni da cewa, yaduwar kwayar cutar kanjamau daga uwa zuwa da ya ragu da kashi uku da rabi bisa dari. Bisa ga wannan nasarar da shirin ya cimma, gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta hakikanta cewa, za a shawo kan matsalar yada kwayar cutar kanjamau daga uwa zuwa jariri baki daya a karshen shekara ta dubu biyu da goma sha biyar. Likitoci suna shirin sake gwajin cikin shekarar nan da kuma shekara ta dubu biyu da goma sha biyu domin su iya gane ainihin nasarar shirin hana daukar kwayar cutar HIV na lokaci mai tsawo.

XS
SM
MD
LG