Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawa Sun Ki Amincewa da Sakamakon Zaben Tanzania


Zabe a Tanzania
Zabe a Tanzania

Babban dan hamayya a zaben da aka yi a Tanzania Edward Lowassa, yayi watsi da sakamkon zaben shugabancin kasar da aka yi, yana zargin anyi magudi.

Lowassa, wanda shugabannin hadakar jam'iyun da suka tsaida suka rufawa baya, yayi magana a wani taro da manema labarai jiya Laraba a birnin Dar es Salaam. Yace bayanai da 'yan hamayya suka tara ya nuna sune suke kan gaba, kamin 'Yansanda su kai samame kan ofishinsu ranar Litinin.

Gwamnati da jam'iyyar CCM mai mulkin kasar ba su ce komi ba nan da nan kan wannan zargi.

Sakamako na baya bayan nan daga hukumar zaben kasar da ta bayyana jiya Laraba ya nuna cewa, Lowassa yana baya ga dan takarar jam'iyyar CCM John Magufuli wand a yake da kashi 59 ciin dari, yayinda Lowassa yake da kashi 40 cikin dari.

Kin amincewar da Lowassa yayi da sakamakon zaben, ya sake jefa rashin tabbas kan zaben musamman domin soke sakamakon zaben daga yankin Zanzibar.

Ahalinda ake ciki kuma, yau Alhamis ne wakilan hukumar zabe a Ghana zasu fara sauraron bayanai daga jam'iyun siyasar kasar da wasu masu ruwa da tsaki wadanda suke neman ganin anyi sabon rijistar kundin sunayen masu zabe.

An ware kwanaki biyu ga jam'iyun su gabatarwa hukumar ra'ayoyinsu dangane da kundin sunayen masu rijista da ake da shi ahalin yanzu. Za'a yi zaman ne a Accra babban birnin kasar.

XS
SM
MD
LG