Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Agajin Kungiyar Izala Sun Samu Horaswa


Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau
Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau

International Committee of Red Cross” ICRC, tare da hadin gwiwar Red Cross sun horas da ‘yan kungiyar Izala

Kungiyar bada agaji mai suna” International Committee of Red Cross” ICRC, tare da hadin gwiwar Red Cross sun horas da ‘yan aikin agaji na kungiyar Izalatul Bidi'a Wa’Iqamatis Sunnah na kasa hanyoyin bada agajin farko wa mutanen da suka samu kansu cikin yanayi tashin hankula da kuma hadarurruka iri daban daban.

Jami’in horas da ‘yan agaji game da dabarun bada taimakon farko Auwal Umar Bashar, yace wannan taro an gudanar da shine da hadin gwiwar kungiyar ICRC, fata na ga wannan taro shinr lalle su dauki wanna horo da suka samu zuwa ga dukkan jahohin su.

Suma jami’an agajin sun bayana horon da suka samu da cewa gaskiya sun koyi abubuwa dayawa cikin aikin agaji daga cikin abubuwa da muka koya mun koyi yadda dan agaji zai shiga inda aka samu hadari kuma ya tsare kansa daga faduwa cikin wannan hadarin kuma ya fido da mutanen da hadarin ya ritsa dasu ya fido su ya basu taimakon farko kafin zuwa Asibiti.

Daga bisani a jawabin sa na godiya shugaban ‘yan agaji na kasa Mustapha Imam Sitti,yace hakika haduwar tana bada fa’ida kwarai bisa halin da ake ciki a wannan kasa tamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

XS
SM
MD
LG