Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Garin Damasak Na Jihar Borno


Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kai wasu hare-hare a wasu cibiyoyi guda uku na kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa a arewa maso gabashin Najeriya.

An kai harin ne ranar asabar da dare, sai dai kawo yanzu, babu wani da ya yi da’awar daukan alhakin kai harin, amma ana zargin kungiyar masu tsatsatsauran ra’ayi da aka fi sani da ISWAP da kai harin.

Kungiyar da ta balle daga kungiyar Boko Haram tana barazana ga ‘yan Najeriya cewa za su kai musu hari muddin suna taimakon kungiyoyin agaji na kasa da kasa a arewa maso gabashin Najeriya.

Daya daga cikin kungiyoyin da aka kaiwa harin ita ce hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Norway, wacce ta ce an lalata motocin da ta ke amfani da su wajan kai kayayyakin agaji ga fararen hula.

Arewa maso gabashin Najeriya ya jima yana fama da matsalar rikicin Boko Haram, lamarin da ya yi sanadin mutuwar daruruwan dubban mutane ya kuma raba wasu miliyoyi da muhallansu.

Karin bayani akan: Jihar Borno, Majalisar Dinkin Duniya, ISWAP​, ‘yan bindiga​, Boko Haram​, Nigeria, da Najeriya.

Hakan ya haifar da miliyoyin 'yan gudun hijira wadanda suke neman mafaka a ciki da wajen jihohin Borno da Yobe da wasu sauran jihohi da ke makwabta da su.

A kwanan nan kungiyar ta Boko Haram ta yi ikirarin harbo wani jirgin saman Najeriya wanda ya bata, ikirarin da rundunar sojin saman Najeriya ta musanta.

Baya ga wannan matsala ta Boko Haram, arewa maso yammacin kasar na kuma fama da matsalar 'yan bindiga da ke kai hare-hare a jihohin Sokoto, Katsina, Zamfara da Kaduna.

Hakan ya haifar da matsalar yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa, lamarin da ya zama ruwan dare a sassan arewacin kasar.

XS
SM
MD
LG