Accessibility links

A Kano Wasu 'Yan Bindiga Sun Kashe Ma'aikatan Kiwon Lafiya 9

  • Aliyu Imam

Wasu makamai da aka kwace a hanun 'yan bindiga.
Wasu yan bindiga da ake zaton yan boko haram ne sun bude wa wasu ma’aikatan kiwon lafiya wuta a arewacin Nigeria, inda suka kashe akallah mutane 9.

Jami’ai sun ce yau ne yan bindigar suka kai harin a wasu wurare biyu a Kano, inda ma’aikatan lafiya ke bada rigakafin cutar shan inna wato polio. Wasu da yawa kuma sun sami rauni sanadiyyar rikicin.

Nigeri na daya daga cikin kasashen duniya kalilan da suka rage inda har yanzu ake fuskantar annobar cutar shan inna. Wannan cutar babbar matsala ce musamman a arewacin Nigeria, inda ake zargin yan boko haram da laifin kai munanan hare-hare.

Wannan kungiya tana da dangantaka da mayakan sa-kan da suke kokarin kafa tafarkin shari’ar musulunci mai tsnani irin tasu fahimtar. Ana azawa kungiyar laifin kisan akalla mutane 3,000.
XS
SM
MD
LG