Accessibility links

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Akalla 25 A Mubi


Kofar shiga cikin Makarantar Fasaha ta Tarayya dake Mubi, Jihar Adamawa, kamar yadda yake kan dandalin makarantar a Intanet.

Hukumomi sun ce ba a san musabbabbin wannan harin da ya kashe mutanen, cikinsu har da dalibai 19 ba, ko kuma yana da nasaba da zaben shugabannin dalibai da aka yi kwanakin baya.

Jami'ai sun ce 'yan bindiga sun kashe mutane akalla 25 a wata unguwar gidajen kwanan dalibai a yankin Arewa maso gabashin kasar.

An kai wannan farmaki cikin daren litinin a wasu gidajen da dalibai na Makarantar Fasaha ta Tarayya dake Mubi a Jihar Adamawa suke kwana.

Kakakin 'yan sanda Mohammed Ibrahim, wanda yayi magana daga birnin Bauchi, ya fadawa Muryar Amurka cewa wadanda suka mutu a wannan harin sun hada da dalibai 19 na Makarantar Fasahar ta Tarayya ta Mubi.

Kungiyar nan ta Boko Haram dai ta sha kai hare-hare a wannan yanki na arewa maso gabas. Amma kuma hukumomi sun ce ba a san musabbabin wannan hari na Mubi ba.

Wani kakakin Hukumar Ayyukan Agajin Gaggawa ta Kasa ta Najeriya, Yusha'u Shu'aib, yace watakila wannan lamarin ya samo asali ne daga harkokin siyasar cikin makarantar a bayan da aka gudanar da zaben shugabannin dalibai.

Shu'aib yace an kai wadanda suka ji rauni a wannan farmaki zuwa asibitocin dake yankin, kuma a yanzu kura ta dan lafa.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG