Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Fansho Sun Gudanar da Zanga-zanga a Filato


Jonah Jang gwamnan jihar Filato

Jihar Filato na cikin jihohin Najeriya da suka kwashe wata da watanni basu biya ma'aikatansu ba lamarin da ya sa 'yan fansho ala tilas suka shiga yin zanga-zanga.

Sun shiga zanga-zangar ne domin su tilastawa gwamnati ta biyasu hakinsu.

Shugaban 'yan fansho na kasa reshen jihar Filato Danladi Jimoh yace 'yan fansho da yawa sun mutu saboda rashin abun biyan bukata. Yawancinsu sun kamu da cutar sikari domin rashin biyan albashi da sauransu. Yace sun sha kai kukansu ga gwamnati amma an ki jinsu. Suna rokon gwamnati ta tausaya masu. Sun ce babu ruwansu da siyasa hakinsu suke nema.

Wasu sun ce da yawansu sun kamu da cuwurwuta kana 'ya'yansu basu da isasshen abinci domin basu da kudi. Abun takaici ne bayan sun yi aiki yanzu an yi watsi dasu. Suna roko kada gwamnati ta mayar dasu kwandon shara. Wata tace tayi shekara biyar ba'a biyata ba.

Shugaban ma'aikatan jihar Ezakiel Dalyop yayi alkawarin cewa nan ba da dadewa ba gwamnati zata biyasu kudadensu. Yace sun zauna dasu. Sun basu haukuri. Sun kaisu gaban manyan kusoshin gwamnati. Yanzu an yi niyya a biyasu kudin wata daya amma kudin bai shiga cikin asusunsu ba a bankunansu. Ya kara da basu hakuri.

Ga rahoton Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG