Wannan lamarin ya auku ne da safiyar yau inda wadanda suka shida lamarin suka fadawa Muryar Amurka cewa sun ga mutanen uku, biyu cikinsu 'yan mata ne dayan kuma namiji ne matashi wanda shekarunsa ba su wuce 20 ba.
Duk 'yan kunar bakin waken sun nufi inda aka ajiye tankunan mai ne suka shiga karkashinsu suka ta da bama-baman da suka yi damara da su.
To sai dai babu wanda ya halaka daga cikin mutanen gari ba ya ga su 'yan kunar bakin waken.
A lokuta da dama, 'yan kunar bakin waken ne kan rasa rayukansu saboda duk wani kokari da suka yi na shiga Maiduguri ya cutura.
Wanmnan shi ne karo na biyar da 'yan kunar bakin waken ke hasarar rayukansu a 'yan kwanakin nan a hare-haren da suke kaiwa a birnin na Maiduguri.
Domin samun karin bayani saurari rahoton da Haruna Dauda ya aiko mana
Facebook Forum